News
Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Fara Hutun Makarantun Firamare Da Sakandare
Ma’aikatar Ilimin Jihar Kano ta sanar da cewa dukkan makarantun firamare da sakandare — na gwamnati da na ƙasar, na kwana da na jeka-ka-dawo — za su rufe zangon farko na karatu a ranar Asabar, 13 ga Disamba, 2025.
A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar, Musbahu Aminu Yakasai, ya fitar, an bukaci iyaye da masu kula da ɗalibai a makarantun kwana da su je su karɓi ‘ya’yansu daga makarantu tun daga Juma’a, 12 ga Disamba, 2025.
Wasu ‘Yan Siyasa Suna Da Hannu A Matsalar Tsaro —Tsohon Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya
Jadawalin Komawa Makaranta
– Ɗaliban makarantun kwana za su koma makarantu a ranar Lahadi, 18 ga Janairu, 2026.
– Ɗaliban jeka-ka-dawo kuwa za su koma a Litinin, 19 ga Janairu, 2026.
Haka kuma jadawalin zangon karatu na gaba ya nuna:
Zangon biyu: 18 ga Janairu, 2026 – 18 ga Afrilu, 2026
Zangon uku: 3 ga Mayu, 2026 – 1 ga Agusta, 2026
Sanarwar ta ƙara da cewa ɗalibai za su yi kwanaki 10 na azumin Ramadan a makarantu kafin a tafi hutun Sallah daga 1 ga Maris zuwa 21 ga Maris, 2026.
Kira ga Iyaye da Masu Kula da Dalibai
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Dr. Ali Haruna Abubakar Makoda, ya yi kira ga iyaye su tabbatar da bin jadawalin da aka amince da shi, tare da ci gaba da ba da haɗin kai ga ma’aikatar. Ya kuma yi wa ɗalibai fatan yin hutu cikin lafiya da albarka.
