Connect with us

News

Wasu ‘Yan Siyasa Suna Da Hannu A Matsalar Tsaro —Tsohon Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya

Published

on

Spread the love

A Najeriya ana ci gaba da zargin wasu ‘yan siyasa da hannu a tashin hankali da matsalar tsaro da ake fama da su a kasar.

Daya daga cikin masu irin wannan zargi shi ne tsohon hafsan hafsoshin tsaron kasar Janar Lucky Irabor, mai ritaya, wanda yayin wata hira da aka yi da shi, ya bayyana cewa matsalolin tsaron da kasar ke fama da su a yanzu haka, na da nasaba da yadda wasu yan siyasar ke daukar nauyin abubuwan da ke faruwa don cimma wata manufa ta siyasa.

Fashewar Tayar Motar Yashi Ta Yi Ajalin Mutum 2 A Kano

Tsohon hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Lucky Irabor ya ce galibin matsalolin tsaron da kasar ke fama da su na da nasaba da yadda wasu ‘yan siyasa ke daukar nauyin wadannan masu kai hare-hare.

A watan Nuwamban da ya gabata ma babban mashawarcin shugaban Najeriya a bangaren sadarwa Daniel Bwala ya ce nan gaba kadan gwamnatin kasar za ta fallasa sunayen masu daukar nauyin ayyukkan ta’addanci.

Advertisement

Masana lamurran tsaro sun ce akwai alamun kamshin gaskiya a wadannan kalamai masu kusanci da juna.

Kalaman tsohon babban hafsan tsaron Najeriyar Janar Lucky Irabor na zuwa a irin wannan lokaci da matsalar tsaro ta dabaibaiye kusan ko’ina a jahohin arewacin kasar, inda a hirarsa da tashar talabijin ta Channels ya yi zargin cewa da yawa a akwai masu shigar burtu a gwamnati, da ke nuna tamkar suna bayar da gudummuwa wajen yaki da matsalar tsaro, amma kuma su ne ruwa su ne tsaki wajen haddasa tashe-tashen hankali masu nasaba da kisa da satar jama’a a fadin kasar.

Akwai dai zarge-zarge masu karfi da masana lamurran tsaro suka dade suna yi na cewa galibin tashe-tashen hankali a shiyyoyin arewa maso gabas da arewa maso yamma na da sa hannun ‘yan siyasa.

A hirarsa da BBC Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin harkokin tsaro na Beacon Security and Intelligence Limited, ya ce akwai shaidu cikakku da suka tabbatar da haka.

Advertisement

Kazalika, wasu ‘yan siyasar Najeriyar sun bayyana cewa ba za a rasa baragurbin masu daukar nauyin ‘yan ta’adda ba.

Sai dai a cewar Sanata Umaru Tsauri ya kamata gwamnati ta fallasa sunayen ‘yan siyasar da ake zargi

Wannan zargin dai na zuwa ne daidai lokacin da galibin jihohin arewacin kasar ke fuskantar farmakin ‘yan bindiga jere da juna.

Abin da ya sa shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu sanya dokar ta-baci a bangaren tsaro inda bayan ajiye aiki da ministan tsaron kasar Muhammad Badaru Abubakar ya yi, cikin kwana daya shugaban ya maye gurbinsa da tsohon hafsan hafsoshin tsaron kasar Janar Christopher Musa mai ritaya, wanda yanzu yake jiran amincewar majalisar dattawan kasar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *