News
Fashewar Tayar Motar Yashi Ta Yi Ajalin Mutum 2 A Kano
Mutane biyu sun rasu bayan fashewar tayar motar ɗiban yashi a Rimin Zakara, ƙaramar hukumar Ungogo ta jihar Kano.
Rahotanni na nuni da cewa wadanda suka rasa ransu sun hadar da Marigayi Abba mai walda da Isiya Muhammad sun rasa rayukansu nan take sakamakon fashewar.
Shaidar gani da ido, Malam Musa Sani, ya shaida wa Arewa Update cewa motar na gyarawa ne, inda aka je wurin saka taya bayan an cika ta da iska.
“Yayin da ake aikin, tayar ta fashe, ta jefa mutanen sama. Daya daga cikinsu ya mutu nan take, ɗayan kuma ya fashe kayan jikinsa suka bulla waje,” in ji Malam Musa.
Ya bayyana cewa al’ummar yankin sun firgita lokacin da aka ji ƙarar fashewar.
Jami’an tsaro daga ofishin ‘yan sanda na Rijiyar Zaki sun iso wurin don bincikar lamarin.
Haka zalika an gudanar Jana’izar su kamar yadda addinin musulunci ya tanada
