Connect with us

News

‎Majalisar Dokokin Jihar Akwa Ibom Ta Ki Amincewa Da Dokar Hana Cin Naman Kare

Published

on

images (6)
Advertisements
ads

Majalisar dokokin jihar Akwa Ibom ta ki amincewa da wani kudiri da ya nemi a haramta cin naman kare a jihar, bayan da babu wani ɗan majalisa da ya mara masa baya yayin zaman majalisar na ranar Talata.

‎Dan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Etinan, Uduak Ekpoufot, shi ne ya gabatar da kudirin. Ya ce dalilin shirin haramta cin naman karnukan shi ne matsalar rashin tsaftar da ake samu a wuraren da ake yanka su, lamarin da ya ce na iya haifar da cututtuka ga masu ci.

Ƙungiyoyin Farar Hula 262 Sun Yi Watsi Da Rahoton Daily Trust Kan “Kano — New Bandits Frontier”

‎Ekpoufot ya jaddada cewa wasu hanyoyin yanka karnukan ba su da tsabta, kuma suna iya jawo cututtuka irin su rabies, salmonella, trichinella da wasu kwayoyin cuta da ke barazana ga  lafiyar jama’a. Ya kuma ce yadda ake kashe karnukan a wasu wurare ba tausayi.

‎Sai dai duk da wadannan hujjojin da ya gabatar, babu wani dan majalisa da ya goyi bayan kudirin, kamar yadda ka’idar majalisa ta tanada kafin a fara tattaunawa.

‎Wani mai taimakawa Gwamna Umo Eno wajen yada labarai, Essien Nduese, ne ya wallafa bayanan zaman majalisar a Facebook, inda ya tabbatar da cewa kakakin majalisar ya yi watsi da kudirin bayan rashin samun mai mara masa baya.

‎Hakan na nufin cewa, cin naman kare a Akwa Ibom zai ci gaba ba tare da wata doka da ke takaita shi ko tsara yadda ake sarrafa shi ba.

Advertisement

 

 

PREMIUM TIMES 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending