Connect with us

News

Jami’an Kwastam Sun Kama Wani Jirgin Ruwan Brazil Ɗauke Da Hodar Iblis A  Lagos

Published

on

Majalisa Ta Kara Adadin Kudin Da Hukumar Kwastam Zata Tara A Shekarar 2025
Spread the love

Hukumar Kwastam, ta kama kilo 25.5 na hodar iblis a wani jirgin ruwa na ƙasar Brazil mai suna MV San Anthonio a tashar jirgin ruwa ta Legas.

Babban jami’in Custom mai kula da tashar jiragen ruwan Emmanuel Oshoba, ya ce an gudanar da aikin ne bayan samun bayanan sirri tare da haɗin gwiwar hukumar yaƙi da sha da fataycin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA.

‎Wani Dattijo Mai Shekara 65 Tare Da Ɗansa Sun Mutu A Cikin Rijiya A Kano ‎

Babban jami’in Ya ƙara da cewa jirgin ya tsaya a ƙasashen da suka yi ƙaurin suna wajen harkar safarar miyagun ƙwayoyi kafin isowarsa Najeriya.

A yayin da aka tsare jirgin, sannan aka kama kuma aka ƙwace hodar tare da miƙa ta miƙa ta ga hukumar ta NDLEA domin ci gaba da bincike.

Advertisement

Oshoba, ya ce wannan nasara tana nuna jajircewar hukumar Kwastam wajen kawar da haramtattun kasuwanci da kuma kare ƙasa, musamman lokacin bukukuwan ƙarshen shekara ke ƙaratowa.

Ya yi gargaɗin cewa hukumar ba za ta bari a yi amfani da ita wajen aikata laifuka ba, kuma duk kayayyakin da suka shigo da su sai an yi bincike a kansu.

A cewarsa, haɗin kai tsakanin Kwastam da NDLEA yana bayar da kyakkyawan sakamako, kuma zai ci gaba da karya tsarin masu safarar miyagun ƙwayoyi.

Jami’an NDLEA ƙarƙashin jagorancin CN Haliru Umar sun karɓi kayan da aka kama.

Advertisement

Kwastam ta kuma buƙaci masu mu’amala da tashar su kasance masu bin doka tare da kai rahoton duk wani abun zargi domin tabbatar da tsaron tashar.

 

 

FRI HAUSA 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *