Connect with us

Politics

Tsohon Ɗan Majalisar Jihar Kano, Zubairu Madobi, Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

Published

on

IMG 20260124 WA0014
Tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano, Honarabul Zubairu Mahmuda Madobi,
Spread the love

Tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano, Honarabul Zubairu Mahmuda Madobi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP).

Hon. Madobi, wanda mamba ne a ma’aikatar kula da ma’aikatan Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar kuma ya rabawa manema labarai a ranar 23 ga watan Janairun 2026.

Gidauniya ta Nemi Haɗin Gwiwa da Ma’aikatar Jin Ƙai don Shirye-Shiryen Ciyawar Ramadan

Advertisement

A cikin sanarwar, Hon. Madobi ya ce ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar NNPP ne bayan tuntubar magoya bayansa tare da la’akari da wasu muhimman dalilai na siyasa.

“Daga ranar 23 ga Janairun 2026 na sanar da ficewata daga jam’iyyar NNPP, bayan tuntubar magoya baya da kuma yin nazari kan wasu dalilai,” in ji shi.

Ya kuma mika godiyarsa ga jam’iyyar bisa damar da ta ba shi na tsayawa takara a zaɓen da ya gabata, yana mai yi mata fatan alheri a dukkan harkokinta na siyasa.

Advertisement

Hakazalika, Hon. Madobi ya jaddada cewa zai ci gaba da bayar da goyon bayansa ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, a duk wani mataki na siyasa da zai ɗauka domin ci gaban jihar.

“Ina tabbatar da ci gaba da goyon bayana ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a kowanne mataki na siyasa da zai ɗauka domin bunƙasa Jihar Kano,” in ji sanarwar.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *