Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Nemi Ƙara Ƙaimi Wajen Wayar da Jama’a Kan Nasarorin Gwamna A Manyan Makarantun Jihar 

Published

on

waiya 1365x2048 1
Spread the love

Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci a ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar yaɗa labarai da jami’an hulɗa da jama’a na manyan makarantu domin inganta yaɗa sahihan bayanai kan manufofi da nasarorin da aka samu a fannin ilimi.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa, inda ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan ƙarfafa daidaito da ingancin bayanan da ake isarwa ga al’umma.

DSS Sun Danka Walida Abdullahi Ga Gwamnan  Jigawa Umar Namadi Danmodi

Advertisement

A cewarsa, ana sa ran haɗin gwiwar zai taimaka wajen inganta fahimtar jama’a game da manufofi da shirye-shiryen gwamnati, musamman waɗanda suka shafi ci gaban manyan makarantu a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Waiya ya ce gwamnatin jihar ta samu gagarumin ci gaba a ɓangaren ilimi, ciki har da gyaran gine-ginen makarantu, samar da sabbin dakunan karatu, inganta kayan koyarwa da horas da ma’aikata.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa, tare da magance matsalolin da suka daɗe suna addabar manyan makarantu mallakin jihar.

Advertisement

Haka kuma, kwamishinan ya buƙaci jami’an hulɗa da jama’a su ƙara ƙwazo wajen bayyana ayyukan gwamnati, yana mai jaddada cewa sadarwa mai inganci na taimakawa wajen tabbatar da cewa al’umma na samun cikakken bayani kan sauye-sauyen da ake aiwatarwa a fannin ilimi.

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da bai wa harkar ilimi fifiko a matsayin ginshiƙin ci gaba mai ɗorewa a Jihar Kano.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *