News
An Buƙaci Fulani Su Yi Rajistar Katin Zaɓe Domin Ƙarfafa Wakilcinsu A Harkokin Dimokuraɗiyya
Ƙungiyar G-13 Abba Gida Gida ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin rajistar Katin Zaɓe zaɓe a yankin Kafin Maiyaki, a wani mataki na ƙarfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya ga al’umma.
Mai ba da shawara ta musamman ga Abba Kabir Yusuf kan harkokin Fulfulde, Hajiya Rukayya Umar, ta yi kira ga al’ummar Fulani da su yi anfani da damar rajistar Katin Zaɓen, tana mai jaddada cewa shiga harkokin Shugaban cin ƙasa hakki ne da alhakin kowane ɗan ƙasa.
Fadar shugaban kasa ta karyata labarin cewa an yi yunkurin sakawa Tinubu guba a abinci
Da take jawabi ga taron al’ummar Fulani a yankin, ta bayyana Katin Zaɓe a matsayin hanyar da ke bai wa ‘yan ƙasa damar amfani da haƙƙinsu na zaɓen shugabanni.
“Ikon zaɓen shugabanni a matakin ƙaramar hukuma, jiha da ƙasa baki ɗaya yana hannun masu zaɓe. Saboda haka, bai kamata kowa ya yi watsi da damar rajista ba,” in ji ta.
Hajiya Rukayya ta kuma buƙaci matan Fulani da su ƙara zage damtse wajen ƙarfafa iyalansu da al’ummarsu su shiga harkokin zaɓe.
A cewarta, ƙaruwa a yawan rajistar Katin Zaɓe daga al’ummar Fulani zai taimaka wajen tabbatar da cikakken wakilci da kuma samun damar shiga tsarin shugabanci yadda ya kamata.
Gangamin wayar da kan da ake gudanarwa wani ɓangare ne na babban shirin da ƙungiyar G-13 Abba Gida Gida ke aiwatarwa domin ƙarfafa rajistar Katin zaɓe a matakin ƙasa da al’umma, musamman a yankunan karkara.
