News
Fadar shugaban kasa ta karyata labarin cewa an yi yunkurin sakawa Tinubu guba a abinci
Fadar shugaban ƙasa ya karyata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa an kama wasu ma’aikatan fadar bisa zargin yunƙurin saka guba a abincin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa, Bayo Onanuga, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya bayyana cewa babu gaskiya a rahotannin da ke cewa an kama ma’aikatan da ke aiki a ɗakin dafa abinci na fadar.
Ɗakin Otal Da Kudin Kwana Daya Kai Kusan Miliyan 130 A Dubai
Sanarwar ta biyo bayan wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, inda ake ikirarin cewa jami’an tsaro sun cafke wasu ma’aikatan bisa wani shiri na saka guba.
Bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a kafin fadar shugaban ƙasar ta fito ta yi bayani.
Onanuga ya buƙaci al’umma da su guji yaɗa labaran da ba a tabbatar da su ba, yana mai jaddada muhimmancin tantance sahihancin labari daga majiyoyin hukuma kafin a yaɗa.
