News
Ɗalibai Miliyan 1.5 Ne Suka Yi Rajistar Jarrabawar UTME A Shekarar 2026
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB) ta bayyanawa ɗalibai da sauran al’umma cewar samun nambar e-PIN ko kuma yadda ake yin rajista saboda jarrabawar UTME za a ƙare yin hakan ne ranar 26 ga Tabrairu 2026.
Hukumar ta bada sanarwa inda take nuna ɗalibai fiye da milyan ɗaya ne suka yi rajistar rubuta jarrabawar shiga manyan makarantu ta shekarar 2026.
Fadar shugaban kasa ta karyata labarin cewa an yi yunkurin sakawa Tinubu guba a abinci
Dokta Fabian Benjamin,mai bada shawara kan harkokin da suka shafi sadarwa na hukumar shi ne ya bayyana hakan ranar Laraba ta makon daya gabata.
Ya ce shi tsarin sayar da e-PINs, lamarin da yake ba mai son yin rajistar jarrabawar ta UTME wa’adin zai ƙare a duk cibiyoyin da ake yi ranar Alhamis 26 ga Fabrairu 2026 da ƙarfe goma sha biyu na rana, yayin da kuma lamarin rajistar waɗanda suka daɗe da sayen e-PIN a cibiyoyin da za a rubuta jarrabawar za’a rufe lamarin rajistar ne ranar Asabar 28 ga Fabrairu 2026.
“Ya zuwa ranar Talata,17 ga Fabrairu 2026, nhukumar ta bada sanarwar da take nuna cewa ɗalibai fiye da milyan ɗaya ne 1.5 suka yi rajistar yin jarrabawar. Budu da ƙari Hukumar tace ana samun damar yin rajisatar ɗalibai 100,000 kowace rana, amma duk da hakan a cibiyoyin rajisatar na faɗin tarayyar Nijeriya lamarin yin rajisatar bai wuce kashi talatin ba.
“Hakan ya nuna da akwai waɗanda suke son yi rajistar jarrabawar da yawa amma basu samu damar yin hakan ba, wato damar da aka basu ta su yi amfani da hakan domin su yi rajistar kamar dai yadda ya jaddada,”.
Hukuma ta ƙara jan kunnen ɗalibai masu son yi rajistar cewar, bata tunanin ko zata ƙara bada wani wa’adi na yin rajisatar, bayan lokacin da aka ƙaiyade ya ƙare.
“Hukar ta JAMB tana tafiyar da ayyukanta kamar yadda doka ta bata damar yi ba tare da saɓawa hakan ba saboda duk hukumomin jarrabawa a Nijeriya sun amince da hakan.
“Yadda hukumar ta tsara tafiyar da lamarin jarrabawar ta ta yi hakan ne domin ta ba sauarn hukumomin shirya jarrabawa da su yi nau’oin jarrabawarsu ba tare da ɓata lokaci ba. Shi yasa hukuma ta ke tunanin zuwa yanzu babu wani matakin da aka ɗauka da ya shafi ƙara lokacin yin rajistar, koda kuwa wasu na da tunanin watakila hukumar ta yi hakan,”.
Sanarwar ta yi kira da ɗalibai da cewar su sayi e-PINs kafin lokacin sayar da shi ya ƙare, daga hakanan kuma sai su zarce zuwa cibiyoyin da ake rajista domin su kammala rajisatarsu.
“Idan kuma ɗalibai ya ce zai bare sai sai kwanaki na ƙarshe hakan zai say a fuskanci matsaloli, ga shi kuma iata hukumar ba zata saurari duk wani lamari na a ƙara wa’adin yin rajistar bayan wa’adin da aka ware ya ƙare.
“Hukumar kamar yadda ta ƙara jaddadawa tana ɗaukar matakan ne domin tabbatar da duk wanda ya cancanci yin raista da rubuta jarrabawar ya smu damar yin hakan musamman ma waɗanda suke buƙatar ganin sun rubuta jarrabawwar wannan shekarar ta 2026, don haka take kira da ɗalibai da kada su ɓatawa kansu lokaci su yi ƙoƙarin yin rajistar”.
