News
Gwamnan Borno Ya Sallami Duk Kwaminishoninsa Nan Take
Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno, ya sallami duk kwamishinoninsa tare da rushe Majalisar Zartawa ta Jihar nan take.
A safiyar Litinin din nan gwamnan ya sanar da matakin, tare da umartar duk tsoffin kwamishinonin da su hannanta kayan gwamnati da ke hannunsuu ga Manyan Sakatarorin ma’aikatunsu zuwa ranar Juma’a 3 ga Afrilu, 2026.
Shugaban NUJ Ya Yaba Da Aikin Kano Correspondents’ Chapel, Ya Kira ‘Yan Jarida Su Kara Hadin Kai
Sakataren Gwamnatin Jihar, Bukar Tijani, na ya fitar da sanarwar, tare da bayanin cewa matakin zai bayar da damar yin sauye-sauye a gwamnati da kuma ba wa masu rike da mukamanin gwamnati damar tsayawa domin neman takararar siyasa.
Gwamnan ya bayyana godiya ta musamman ga kwamishinonin da wa’adinsu ya ƙare, bisa jajircewa, sadaukarwa da muhimmiyar gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar da kuma hidima ga al’ummar Borno.
A cewar gwamnan, ƙoƙarin da suka yi ya taimaka wajen inganta ayyukan gwamnati da kuma kawo sauyi ga rayuwar jama’a. Ya kuma yi fatan sabon kwamishinonin da za su karɓi aiki za su ci gaba da gina kan nasarorin da aka samu.
