News
”Yawaitar Yaɗuwar Cututtuka A Cikin Al’umma Na Da Alaƙa Da Rashin Tsaftar Muhalli” —Sarkin Tsaftar Kano
Sarkin Tsaftar Kano, Jamilu Ahmad Gwarzo, ya yi gargadin cewa rashin tsaftar muhalli na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa yawaitar cututtuka a tsakanin al’umma.
A wata tattaunawa da ya yi da Muhasa TV/ Radio, Gwarzo ya bayyana cewa gurbacewar muhalli, musamman a wuraren da jama’a ke rayuwa cikin cunkoso, na kara haddasa cututtuka masu yaduwa, ciki har da gudawa da zazzabin cizon sauro.
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargadi Game Da Yiwuwar Fuskantar Ambaliyar Ruwa A Jihohi 10
Ya ce zubar da shara a wuraren da bai dace ba, da kuma toshe magudanan ruwa, na daga cikin matsalolin da ke janyo tabarbarewar muhalli da kuma barazana ga lafiyar jama’a.
“Yawan cututtuka da ake gani a yau na da alaka kai tsaye da yadda ake kula da muhalli. Idan babu tsafta, to akwai babbar barazana ga lafiya,” in ji shi.
Gwarzo ya bukaci jama’a da su dauki matakan tsaftace muhalli a matsayin wani muhimmin mataki na kariya daga cututtuka, yana mai jaddada cewa tsafta nauyi ne na kowa, ba wai na gwamnati kadai ba.
Haka kuma ya yi kira ga hukumomi da su kara kaimi wajen wayar da kan al’umma tare da samar da ingantattun hanyoyin kula da shara domin rage barazanar cututtuka.
Masana lafiya dai sun dade suna jaddada muhimmancin tsaftar muhalli a matsayin daya daga cikin hanyoyin dakile yaduwar cututtuka a cikin al’umma.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
