Connect with us

News

‎”Yawaitar Yaɗuwar Cututtuka A Cikin Al’umma Na Da Alaƙa Da Rashin Tsaftar Muhalli” ‎ ‎ ‎—Sarkin Tsaftar Kano

Published

on

waste shara
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

‎Sarkin Tsaftar Kano, Jamilu Ahmad Gwarzo, ya yi gargadin cewa rashin tsaftar muhalli na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa yawaitar cututtuka a tsakanin al’umma.

‎A wata tattaunawa da ya yi da Muhasa TV/ Radio, Gwarzo ya bayyana cewa gurbacewar muhalli, musamman a wuraren da jama’a ke rayuwa cikin cunkoso, na kara haddasa cututtuka masu yaduwa, ciki har da gudawa da zazzabin cizon sauro.

‎Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargadi Game Da Yiwuwar Fuskantar Ambaliyar Ruwa A Jihohi 10

‎Ya ce zubar da shara a wuraren da bai dace ba, da kuma toshe magudanan ruwa, na daga cikin matsalolin da ke janyo tabarbarewar muhalli da kuma barazana ga lafiyar jama’a.

‎“Yawan cututtuka da ake gani a yau na da alaka kai tsaye da yadda ake kula da muhalli. Idan babu tsafta, to akwai babbar barazana ga lafiya,” in ji shi.

‎Gwarzo ya bukaci jama’a da su dauki matakan tsaftace muhalli a matsayin wani muhimmin mataki na kariya daga cututtuka, yana mai jaddada cewa tsafta nauyi ne na kowa, ba wai na gwamnati kadai ba.

Advertisement

‎Haka kuma ya yi kira ga hukumomi da su kara kaimi wajen wayar da kan al’umma tare da samar da ingantattun hanyoyin kula da shara domin rage barazanar cututtuka.

‎Masana lafiya dai sun dade suna jaddada muhimmancin tsaftar muhalli a matsayin daya daga cikin hanyoyin dakile yaduwar cututtuka a cikin al’umma.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending