Connect with us

News

Gwarzo ya yi alhinin rasuwar fitaccen ɗan jarida Saleh Ashaka

Published

on

1777968466158

Shugaban rukunin jami’o’in MAAUN, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya bayyana rasuwar tsohon wakilin VOA kuma fitaccen ɗan jarida, Saleh Shehu Ashaka, a matsayin babban rashi ba ga harkar yaɗa labarai kaɗai ba har ma ga ƙasa baki ɗaya.

Farfesa Gwarzo ya ce marigayin ya rayu rayuwa mai cike da tasiri da hidima, inda ya sadaukar da aikinsa wajen tabbatar da ƙa’idoji da ƙwarewar aikin jarida. Ya bayyana shi a matsayin jajirtaccen ɗan jarida wanda aikinsa ya sa ya samu girmamawa a faɗin ƙasa da ma ƙetare.

Advertisement

“Kishin Jihar Kano Shine Tabbatar Da Tsaronta” Dole Ne A Kawar Da Siyasar Daba

“Saleh ba kawai ƙwararren ɗan jarida ba ne, har ma mai taimakon jama’a ne wanda ya shafi rayuwar mutane da dama. Yawan saƙonnin ta’aziyya daga sassa daban-daban na ƙasar nan na nuna irin kyawawan halayensa na tausayi, tawali’u da karamci,” in ji shi.

Advertisement

Ya ƙara da cewa Ashaka na daga cikin fitattun wakilan VOA, wanda aka san shi da nutsattsen murya mai kwantar da hankali da kuma salon rahoto mai adalci, lamarin da ya sa ya samu karɓuwa a wajen masu sauraro tsawon shekaru.

Gwarzo ya ce rasuwar marigayin ta haifar da giɓi mai girma da zai yi wuya a cike, musamman a wannan lokaci da masana’antar yaɗa labarai ke buƙatar gogaggun muryoyi masu ƙa’ida.

Advertisement

Ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalai, abokai da abokan aikin marigayin, tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, Ya kuma ba waɗanda ya bari haƙurin jure wannan babban rashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending