Connect with us

News

ZAƁEN 2027: Bayan Shugaba Tinubu ƴan Takarar Shugaban Ƙasa 7 Ne Suka Fito Daga Kudancin Najeriya

Published

on

‎Yayin da shirye-shiryen babban zaɓen shekarar 2027 ke ƙara ɗaukar zafi a Najeriya, alamu na nuna cewa yankin Kudancin ƙasar ne ya mamaye fagen neman kujerar shugaban ƙasa, inda baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wasu fitattun ‘yan siyasa bakwai daga yankin suka bayyana a matsayin masu neman tikitin shugabancin ƙasa ta jam’iyyu daban-daban.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya riga ya samu tikitin jam’iyyarsa domin neman wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

NUT Ta Yi Barazanar Rufe Makarantu A Najeriya Saboda Matsalar Tsaro

‎A ɓangaren adawa kuwa, tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya bayyana a matsayin ɗan takarar jam’iyyar Nigeria Democratic Congress.

‎Haka kuma gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya shiga takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar Allied People’s Movement.

‎Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, shi ma ya bayyana a matsayin ɗan takarar wani ɓangare na jam’iyyar People’s Democratic Party, duk da ci gaba da rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar.

Advertisement

‎A jam’iyyar Social Democratic Party kuwa, an tsayar da Adewole Adebayo a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa bayan ya samu amincewar wakilan jam’iyyar a taronta na ƙasa.

‎Sauran waɗanda suka shiga fafatawar sun haɗa da tsohon gwamnan Jihar Cross River, Donald Duke na jam’iyyar People’s Redemption Party, da kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore na jam’iyyar African Action Congress.

‎Rahotanni sun kuma nuna cewa Anita Zugwai-Chukwu na daga cikin ‘yan takarar jam’iyyar Young Progressives Party da suka bayyana a fafatawar 2027.

‎Masana harkokin siyasa na ganin cewa yawaitar ‘yan takara daga Kudancin Najeriya na iya haifar da rarrabuwar ƙuri’un adawa, lamarin da zai iya sauya yanayin fafatawar zaɓen 2027 idan har ba a samu haɗin kai tsakanin manyan jam’iyyun adawa ba kafin lokacin zaɓe.

Jerin Jam’iyyu Da ‘Yan Takararsu

Advertisement

‎APC — Bola Ahmed Tinubu

‎NDC — Peter Obi

‎APM — Seyi Makinde

Advertisement

‎PDP — Goodluck Jonathan

‎SDP — Adewole Adebayo

‎PRP — Donald Duke

Advertisement

‎AAC — Omoyele Sowore

‎YPP — Anita Zugwai-Chukwu

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending