News
Ana Dab Da Kafa ’Yansandan Jihohi — Fadar Shugaban Ƙasa
Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba a yunkurin kafa rundunar ’yan sandan jihohi, lamarin da ke nuna cewa Najeriya na ƙara matsowa kusa da aiwatar da tsarin da aka daɗe ana tattaunawa a kansa.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan bayan wani taron tuntuba da ya haɗa bangaren zartarwa, Majalisar Dokoki ta Ƙasa da shugabannin hukumomin tsaro a Abuja.
Yadda Tashar Talabijin Mallakin Gwamnatin Kano Ta Zama Cibiyar Sare Bishiyu Da Sayar Da Itace
Ya ce tattaunawar kafa ’yan sandan jihohi ta samu gagarumin ci gaba ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda a yanzu ake duba yiwuwar yin gyaran kundin tsarin mulki da sauran dokokin da za su ba da damar aiwatar da tsarin.
A cewarsa, mafi yawan masu ruwa da tsaki sun amince cewa lokaci ya yi da za a samar da rundunar ’yan sandan jihohi domin ƙarfafa matakan tsaro a matakin jihohi da ƙananan hukumomi.
“Yanzu dai muhawarar ba ta kan ko za a kafa ’yan sandan jihohi ko a’a ba ce, sai dai yadda za a tsara dokoki da matakan gudanarwa da za su tabbatar da inganci da kauce wa matsalolin da ka iya tasowa,” in ji shi.
Gbajabiamila ya ƙara da cewa za a miƙa cikakken rahoton taron ga Shugaba Tinubu domin ya yi nazari tare da ɗaukar matakan da suka dace.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da tattaunawa da sassa daban-daban na ƙasa domin samar da tsarin da zai taimaka wajen inganta tsaro, ƙarfafa tattara bayanan sirri da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Batun kafa ’yan sandan jihohi dai na daga cikin manyan batutuwan da suka daɗe suna jawo muhawara a Najeriya, inda masu goyon baya ke ganin zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi sassa da dama na ƙasar.
