Connect with us

News

Kotu Ta Umarci Hukumar  INEC Ta Yi Wa Jam’iyyar Access Party Rajista

Published

on

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta ci gaba da aiwatar da tsarin yi wa Jam’iyyar Access Party (AP) rajista, tare da ba ta damar kammala dukkan matakan da suka dace domin samun sahalewar aiki a matsayin jam’iyyar siyasa a Najeriya.

Mai Shari’a Obiora Atuegwu Egwuatu, yayin yanke hukuncin ranar Laraba, ya bayyana cewa matakin da INEC ta ɗauka na dakatar da aikin rajistar jam’iyyar ya saɓa wa tanade-tanaden doka.

Advertisement

Kotun ta ce bayan nazarin hujjojin da ɓangarorin biyu suka gabatar, ta gamsu cewa tambarin da Access Party ta gabatar ya cika dukkan sharuɗɗan da doka ta tanada, don haka babu wata hujja da za ta hana ta ci gaba da neman rajista.

An shigar da ƙarar ne ta hannun lauyoyi Audu Bulama Bukarti da Mevon Samuel, waɗanda suka wakilci jam’iyyar bayan INEC ta dakatar da tsarin rajistarta a watan Satumban 2025. Hukumar ta yi iƙirarin cewa akwai kamanceceniya tsakanin tambarin da jam’iyyar ta zaɓa da wasu tambura.

Advertisement

Sai dai kotun ta yi watsi da wannan hujja, inda ta umurci INEC da ta dawo da tsarin rajistar jam’iyyar ba tare da wani ƙarin tsaiko ba.

Haka kuma, kotun ta umarci INEC da ta biya masu ƙarar tarar Naira 500,000 a matsayin diyya.

Advertisement

Masu bibiyar harkokin siyasa sun bayyana hukuncin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa dimokaraɗiyya da tabbatar da ‘yancin ‘yan ƙasa na kafa jam’iyyun siyasa da shiga harkokin mulki bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending