News
An Zargi Direban Jirgin Air Canadda Tuka Jirgin Sama Tsawon Shekaru 17 Da Lasisin Bogi
Wani tsohon kyaftin ɗin jirgin saman kamfanin Air Canada, Geoffrey Wall, ya shiga hannun hukuma bayan da ake zarginsa da amfani da takardun lasisin tukin jirgin sama na bogi tsawon shekaru da dama.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan sanda a yankin Peel da ke lardin Ontario na ƙasar Canada sun kama Wall mai shekaru 59 bayan kammala bincike na tsawon watanni huɗu kan zarge-zargen da ake masa.
Gwamnatin Tarrayya Ta Ware Naira Bilyan 10 Domin Dakike Barazanar Cutar Ebola
A cewar hukumomin tsaro, an gurfanar da shi a gaban kotu kan laifukan damfara da wasu tuhume-tuhume masu alaƙa da harkokin sufurin jiragen sama.
Binciken ya nuna cewa Wall ya jagoranci sama da jirage 900 na cikin gida da na ƙasashen waje tsakanin shekarun 2009 zuwa 2025, inda ake zargin ya yi hakan ne ta amfani da lasisin da ba sahihi ba.
Hukumomi sun bayyana cewa duk da kasancewarsa mai ingantaccen lasisin tukin jirgin sama na kasuwanci, ba shi da lasisin Airline Transport Pilot Licence (ATPL), wanda shi ne mafi girman matakin lasisin da ake buƙata domin mutum ya zama kyaftin ɗin jirgin sama.
Lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce a fannin sufurin jiragen sama, yayin da masu ruwa da tsaki ke tambayar yadda aka yi aka kasa gano wannan gibi na tsawon shekaru masu yawa.
A halin yanzu, hukumomin Canada na ci gaba da gudanar da bincike domin gano yadda aka samu wannan tangarda da kuma ko akwai wasu da suka taka rawa wajen ba shi damar ci gaba da aiki ba tare da an gano matsalar ba.
