Connect with us

News

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamnan Kano Da Grandi Khadi Akan Alaƙalin Hukumar Hisba Sani Tanimu

Published

on

IMG 20260611 WA0007

Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu 

Ya mai girma gwamna Kano mai adalci Alh Abba Kabir Yusuf da shugaban alkalan kotunan shari’ar Musulunci ta jihar kano Dr Tijjani Yusuf Yakasai ina muku fatan alheri Allah ya kara muku lafiya da kwanciyar hankali ameen.

Advertisement

Mai girma Gwamna da Grandi Khadi na rubuta wannan takardar ne aka alkalin Hukumar Hisba Sani Tanimu kan rashin adalci da yake yi a aikin sa, tare da nuna son zuciya da bangaranci yayin gabatar da Shari’a kamar yadda mahaifiyar wata yarinya tayi mana korafi.

ZARGIN KWACE GONAKI: An Kai Sarkin Rano Da Karamar Hukumar Bunkure Kara Kotu

Advertisement

Akwai wasu yara mata da suka yi rikici tsakanin su, har suka fada zuwan zafi, hakan ya janyo wadda tafi konewar matar aure ce zata kai shekara 20 ko kusa da haka, abokiyar fadan kuma zata kai shekaru 17, hakan ya janyo har Police station aka kai case din, mijin matar da iyayenta suka hakura amma, wani fitinnen tsohon Alkali mai suna Idris Yahya ana masa laƙabi da Mai Hannu Ɗaya dan unguwar Sheka wanda yake a matsayin sirikin mijin yarinyar yace bai hakura ba, saboda wasu dalilai nasa!

Haka aka ajiye yarinyar nan ta kwana a tsare, washe gari aka kaita Kotun hisba, wanda Kafin aje shi wannan tsohon alkalin mai hannu daya wato Idris Yahya ya shirya da an je a daure yarinyar saboda yana da alaƙa da alkalin.

Advertisement

Ana zuwa kuwa shi Alkalin Hisba ya tura yarinyar gidan gyaran hali zuwa tun ranar Alhamis sai ranar Litinin, anyi anyi a bada beli duba da ƙarancin shekarunta da kuma cewar fada suka yi tare, amma ya kekasa kasa yaƙi duk don farantawa shi wannan tsohon alkalin saboda mai gidan sane.

Da aka dawo Litinin ta daga ita sai sallah Babba ya sake mai da yarinyar nan gidan gyaran hali sai da ta kara kwana 11 a rufe, sai jumaat 5 ga wata aka bada belin ta da kyar

Advertisement

Don haka ne mai girma gwamna da grandi Khadi Mahaifiyar wannan yarinyar tace bata da wani gata sai Allah sai ku, tace bata da hanyar garinku amma jaridar Alfijir ta sanar da ku domin a nemawa yarinyarta hakkin wannan kin zarafin da tsohon alkalin Idris Yahya ya saka Alkalin Hisba Sani Tanimu yayi musu.

Ina muku fatan alheri Allah ya sa a gama lafiya.

Advertisement

 

Editan Jaridar Alfijir Labarai

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending