Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Wata Mata Bisa Zargin Saran Mijinta Da Adda

Published

on

Adda 1

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo ta gurfanar da wata matar aure a gaban kotu bisa zargin saran mijinta da adda, lamarin da ya haddasa masa mummunan rauni a hannun hagu.

Kakakin rundunar, DSP Abayomi Jimoh, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 2 ga watan Yunin 2026 da misalin karfe 2:30 na dare bayan wata takaddama ta barke tsakanin ma’auratan.

Advertisement

Dakarun Soji Sun Kubutar Da Matar Marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar Daga Hannun ’Yan Bindiga.

A cewarsa, matar da ake zargin ta kai wa mijinta, Olatunde Julius, hari da adda yayin rikicin, wanda ya yi sanadin raunata shi.

Advertisement

 

Jimoh ya ce an garzaya da wanda abin ya shafa zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci, inda aka tantance raunukan da ya samu tare da rubuta rahoton likita da zai taimaka wajen gudanar da bincike.

Advertisement

Ya kara da cewa bayan kammala bincike, rundunar ta gano cewa akwai hujjojin da suka isa a gurfanar da matar a gaban kotu domin fuskantar tuhumar da ake yi mata.

Kakakin ya jaddada cewa rundunar ’yan sanda ba za ta lamunci duk wani nau’in cin zarafin cikin gida ba, yana mai cewa irin wadannan laifuka na barazana ga rayuka da zaman lafiyar al’umma.

Advertisement

Ya kuma bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani lamari da ya shafi cin zarafi ko tashin hankali cikin gida ga hukumomin tsaro domin daukar matakin da ya dace cikin gaggawa.

Aminiya ta ruwaito cewa, rundunar ta sake nanata kudirinta na tabbatar da adalci ga duk wadanda suka fada cikin irin wadannan matsaloli ba tare da la’akari da jinsi ko matsayin wanda abin ya shafa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending