News
Shugaban FCAPT: Rajistar Katin Zaɓe Muhimmin Mataki Ne Wajen Ƙarfafa Dimokuraɗiyya

Shugaban riko na kwalejin koyon aikin noma ta tarayya dake nan Kano, wato na Federal College of Agricultural Produce Technology (FCAPT), Dr. Salisu Salisu, ya yabawa Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Kano da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) bisa yadda suke gudanar da aikin Sabunta Rajistar Masu Zaɓe (CVR) cikin tsari da lumana.
Dr. Salisu ya bayyana hakan ne yayin da ake gudanar da aikin rajistar katin zaɓe a kwalejin, ƙarƙashin kulawar Kwamitin Kar-ta-Kwana kan Rijistar Katin Zaɓe (CVR) da gwamnatin jihar ta kafa domin ƙara kusantar da aikin ga al’umma.
Saurin Wallafa Labari Ba Shi Ne Ke Samar Da Amincewar Jama’a Ba — Shugaban NUJ
Ya ce matakin da gwamnatin ta ɗauka na kai aikin rajistar zuwa cibiyoyin ilimi da sauran wuraren taruwar jama’a ya sauƙaƙa wa ɗalibai da ma’aikata damar yin rajista da sabunta katunansu ba tare da wata wahala ba.
Shugaban kwalejin ya ce abin alfahari ne yadda ake gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali da tsari, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewar hukumomin da abin ya shafa wajen tabbatar da cewa kowane ɗan ƙasa ya samu damar shiga cikin tsarin dimokuraɗiyya.
Hakazalika, ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa hangen nesansa na kafa Kwamitin Kar-ta-Kwana kan Rijistar Katin Zaɓe (CVR), yana mai cewa wannan mataki ya taimaka matuƙa wajen wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa su su fito domin yin rajista.
Haka kuma ya miƙa godiyarsa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, da Hukumar INEC bisa haɗin gwiwar da suke yi wajen tabbatar da nasarar aikin rajistar.
A ƙarshe, Dr. Salisu ya yi kira ga ɗalibai, ma’aikata da sauran al’umma da su yi amfani da wannan dama wajen yin rajistar katin zaɓe ko sabunta bayanansu kafin wa’adin da INEC ta ƙayyade ya ƙare.
