News
Saurin Wallafa Labari Ba Shi Ne Ke Samar Da Amincewar Jama’a Ba — Shugaban NUJ

Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahya, ya buƙaci ‘yan jaridun yanar gizo da su ba da fifiko ga gaskiya, sahihancin labarai da bin ƙa’idojin aikin jarida, yana mai jaddada cewa amincewar jama’a ba ta ginu ne kan saurin wallafa labari ba, illa ingancinsa da gaskiyarsa.
Shugaban na NUJ ya bayyana haka ne a jawabin da Kwamared Abbas Ibrahim, Amintaccen Ɗan Kwamitin Amintattu na Ƙasa mai kula da Shiyya ta A, ya gabatar a madadinsa yayin bikin ƙaddamar da Online Chapel na NUJ reshen Jihar Jigawa, wanda aka gudanar ranar Talata a Cibiyar ‘Yan Jarida ta NUJ da ke Dutse.
Ya taya shugabanni da mambobin sabon chapel ɗin murnar cika dukkan sharuddan da kundin tsarin mulkin ƙungiyar ya tanada, yana mai cewa hakan ya nuna jajircewarsu wajen inganta aikin jarida da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin ‘yan jarida.
A cewarsa, ci gaban fasahar zamani ya sauya yadda ake gudanar da aikin jarida, inda kafafen yanar gizo suka zama muhimman hanyoyin yaɗa labarai, wayar da kan jama’a da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya.
Ya ce kafafen yanar gizo suna bai wa ‘yan jarida damar isar da labarai cikin gaggawa, kai rahotanni ga masu karatu a sassa daban-daban na duniya, tare da amfani da hotuna, bidiyo, sauti da sauran dabarun zamani wajen gabatar da labarai.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa waɗannan damammaki na zuwa ne tare da ƙalubale, ciki har da yaɗuwar labaran ƙarya, bayanan da ba a tantance ba, satar ayyukan wasu da kuma matsin lambar wallafa labarai cikin gaggawa ba tare da cikakken bincike ba.
Ya ce, “A matsayinku na mambobin NUJ, ku jakadu ne na gaskiya da riƙon amana. Ku tabbatar da sahihancin duk wani bayani kafin wallafawa, ku mutunta mutunci da sirrin jama’a, ku guji kalaman ƙiyayya, sannan ku tabbatar da cewa adalci, daidaito da ingantaccen rahoto su ne ginshiƙan aikinku.”
Ya ƙara da cewa makomar aikin jarida ta yanar gizo za ta dogara ne da yadda masu sana’ar za su kiyaye ƙa’idojin aiki da kuma kare amincewar da jama’a suka ɗora musu.
Shugaban ya kuma tabbatar da cewa Sakatariyar Ƙasa ta NUJ za ta ci gaba da shirya horaswa da sauran shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewar ‘yan jaridun yanar gizo domin tabbatar da cewa aikin jarida na dijital a Najeriya ya kasance abin koyi a matakin ƙasa da ƙasa.
Ya kuma buƙaci mambobin sabon chapel ɗin da su kasance masu haɗin kai, su kare ‘yancin aikin jarida, su rungumi ɗa’a da ƙwarewa, tare da bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa ta hanyar wallafa sahihan labarai masu amfani ga al’umma.
An kammala taron ne da ƙaddamar da Online Chapel na NUJ reshen Jihar Jigawa, wanda ake sa ran zai ƙara bunƙasa aikin jarida na yanar gizo a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.
