News
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mutane Biyu Kan Zargin Fashi da Makami A Bauchi
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta sanar da cafke wasu matasa biyu da ake zargi da hannu a wani hari na fashi da makami da kuma shiga gida ba tare da izini ba a garin Gadau.
A cewar rundunar, waɗanda ake zargin tare da wasu abokan aikinsu da har yanzu suke gudun hijira, sun kutsa cikin wani gida da misalin ƙarfe 3:00 na dare, ɗauke da adduna da sauran makamai masu haɗari.
Gobara Ta Lalata Dukiyar Naira Miliyan 120, An Ceto Ta Naira Miliyan 481.8 A Kano
Rahoton ya ce maharan sun yi wa maigidan gidan da matarsa barazana, inda suka ɗaure su kafin su kwashe kayayyaki da kuɗaɗe masu yawa. Daga cikin abubuwan da aka sace akwai babur guda ɗaya, wayoyin hannu biyar, atamfofi goma, kuɗi Naira miliyan ɗaya, hula guda ɗaya da agogon hannu guda uku.
Rundunar ta bayyana cewa an kiyasta jimillar darajar dukiyar da aka sace ta kai kusan Naira miliyan huɗu.
Bayan samun rahoton aukuwar lamarin, jami’an ‘yan sanda sun gaggauta fara bincike, wanda ya kai ga cafke mutane biyu da ake zargi da hannu a aikata laifin, yayin da ake ci gaba da farautar sauran waɗanda suka tsere.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin cikin nasara, tare da umartar a ƙara zage dantse wajen bincike domin kamo sauran waɗanda ake zargi.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa wajen dakile aikata laifuffuka da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a faɗin jihar.
