News
Gwamnatin Legas Ta Kama Mabarata Sama Da 390
Gwamnatin jihar Legas a kudu maso yammacin Nijeriya ta kama mabarata 396 kuma ta fara tantance su da zummar mayar da su jihohin da suka fito.
Kwamishinan Muhalli da Albarkatun Ruwa na jihar, Tokunbo Wahab ne ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Talata.
Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Yin Bincike Kan Ma’aikatar Bogi Da Ake Ta Takaddama A Kai
Gwamnatin ta ce waɗanda aka kama ɗin za su samu tallafin da ya dace idan akwai buƙatar hakan kafin a miƙa su ga hukumomin da suka dace domin mayar da su cikin aminci.
Kwamishinan ya ƙara da cewa jami’an rundunar tsaftace muhalli ta jihar Legas (LAGESC) ne suka yi kamen a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na tsaftace jihar da kuma daƙile yin ba daidai ba.
Ya ƙara da cewa aikin wata alama ce ta ƙoƙarin da gwamnatin jihar ke yi na magance matsalar bara a kan tituna da sauran harkokin da ta ke ganin suna zagon ƙasa ne ga tsafatace muhalli da kuma doka da oda.
Sanarwar ta da kwamishinan ya fitar tana tare ne da wani bidiyo da ke nuna gomman waɗanda aka kama ciki har da maza da mata da ƙananan yara da ma masu nakasa.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News4 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
