News
Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Yin Bincike Kan Ma’aikatar Bogi Da Ake Ta Takaddama A Kai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bai wa hukumar ICPC umarnin gudanar da bincike kan badaƙalar ma’aikatar bogin nan ta PFIPC da ake ta taƙaddama akai.
Wannan dai ya biyo bayan caccaka da gwamnatin ke ci gaba da sha daga ƴan adawa da ƙungiyoyin fararen hula da kuma ƴan Najeriya, kan yadda ake zargin wata ma’aikata na wanzuwa ba tare da sanin gwamnati ba.
An samar da shafin Facebook mai suna “Tsaro da Shari’a” domin kawo sahihan labaran Tsaro da Shari’a.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar yau Talata, Tinubu umarci gudanar da binciken tare da miƙa masa rahotansa cikin kwanaki 30.
Wani mutum Adeniyi Adeyimi Mattew ne ya ayyana kansa a matsayin babban daraktan wannan ma’aikata ta PFIPC da ke haɓaka hulda da zuba jari daga ƙasashen waje.
Cikin zarge-zargen da ICPC za ta bincika sun haɗa da yadda Adeyemi ya samu takardar naɗa shi shugabancin ma’aikatar da kuma sauran takardu na hukumomin gwamnati.
Akwai kuma batun yin amfani da muƙamin wajen samun karbuwa a hukumace tare da samun tallafin jami’an diflomasiyya, ciki har da batun takardun biza da buɗe asusun bankin ta hanyar amfani da takardun gwamnati na ƙarya.
Tinubu ya umarci dukkan ma’aikatu da hukumomi da rassa na gwamnatin tarayya da su bai wa ICPC bayanan da suke dasu, wanda zai taimaka mata a binciken.
Shugaban Najeriya ya kuma ce duk wanda aka samu da hannu a wannan badaƙala to zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News4 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
