News
Gobara Ta Lalata Dukiyar Naira Miliyan 120, An Ceto Ta Naira Miliyan 481.8 A Kano
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta bayyana cewa ta yi nasarar ceto dukiyar da darajarta ta kai Naira miliyan 481.8 yayin da gobara ta lalata kadarorin da suka kai kusan Naira miliyan 120.45 a cikin watan Yunin 2026.
Rahoton ayyukan hukumar na watan Yuni, wanda Jami’in Hulɗa da Jama’a, Saminu Yusuf Abdullahi, ya fitar, ya nuna cewa jami’an kashe gobara sun amsa kiraye-kirayen gobara guda 30 a sassa daban-daban na jihar cikin watan.
Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Jami’in Gwamnatin China Hukuncin Kisa Kan Badakalar Cin Hanci
Rahoton ya ce baya ga ayyukan kashe gobara, hukumar ta gudanar da ayyukan ceto guda bakwai a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar, sannan ta karɓi kiran gaggawa guda ɗaya wanda daga baya aka tabbatar cewa ba na gaskiya ba ne.
A cewar rahoton, mutane biyar sun rasa rayukansu sakamakon wasu daga cikin abubuwan da suka faru a watan, yayin da jami’an hukumar suka yi nasarar ceto mutum uku cikin gaggawa.
-
News7 days ago
Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Kai Ziyarar Ba Zata Asibitin Kwararru Na Best Choice Dake Kano
-
Uncategorized3 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days ago
El-Rufa’i Ya Shigar Da Ƙarar Neman Diyyar Biliyan N10 Bisa Zargin ICPC Da Nesanta Shi Da Iyalansa
