Connect with us

News

BA MALAMI A MAAUN BANE: MAAUN Ta Nesanta Kanta Da Tsohon Malami Da Ake Zargi Da Kokarin Cin Zarafin Ɗaliba

Published

on

images (7)

Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN) ta bayyana cewa ba ta da wata alaƙa da wani tsohon malami Dr Nasa’i Gwadabe, da ake alaƙanta da zargin neman cin zarafin wata ɗaliba, tana mai jaddada cewa ya daina aiki da jami’ar tun kafin batun ya bayyana a kafafen sada zumunta.

A cikin wata sanarwa da Magatakardar jami’ar, Habibu Awaisu, ya sanya wa hannu ranar Alhamis, MAAUN ta ce kwantiragin aikin Dr Gwadabe na shekara guda a matsayin malamin ziyara ya ƙare ne a watan Mayun 2026, kuma ba a sabunta masa ba.

Shugaba Tinubu Ya Miƙa Wa Majalisar Dattawa Ƙudirin Gyaran Dokar Ilimin Makarantun Sakandare

Sanarwar ta ce tun daga lokacin ya daina kasancewa ma’aikacin jami’ar, saboda haka bai dace a ci gaba da bayyana shi a matsayin malamin MAAUN ba.

“Hukumar gudanarwar jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria na son fayyace rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta game da Dr Nasa’i Gwadabe. Wa’adin aikinsa na shekara guda ya ƙare a watan Mayun 2026 kuma ba a sabunta masa ba. Saboda haka, ba shi da wata alaƙa da MAAUN a halin yanzu,” in ji sanarwar.

Jami’ar ta bayyana cewa ana ɗaukar malaman ziyara ne bisa kwantiragin shekara guda, wanda sabunta shi ke dogara da buƙatar jami’a, gamsuwar gudanarwa da kuma yadda malamin ya gudanar da aikinsa.

Advertisement

Ta ƙara da cewa kwantiragin Dr Gwadabe ya ƙare ne tare da na wasu malaman ziyara da dama a lokaci guda.

Wannan bayani ya biyo bayan rahotannin da suka bazu a kafafen sada zumunta, inda ake zargin tsohon malamin da yin wasu kalamai da kuma yunƙurin neman lalata da wata ɗaliba.

Sai dai jami’ar ta jaddada cewa lokacin da batun ya fito fili, mutumin da ake zargin ba ya cikin ma’aikatanta, saboda haka bai kamata a haɗa lamarin da jami’ar ba ko a bayyana shi a matsayin malamin jami’ar.

MAAUN ta sake jaddada manufar rashin lamuntar cin zarafi

Jami’ar ta ce tana ci gaba da aiwatar da manufar rashin lamuntar duk wani nau’i na cin zarafi, musamman cin zarafin da ya shafi lalata, tare da ɗaukar matakan kare ɗalibai da tabbatar da adalci.

A cewarta, wanda ya kafa jami’ar ya ware lada ta Naira miliyan biyar (₦5,000,000) ga duk wata ɗaliba da ta kai rahoton cin zarafin lalata ko yunkurin hakan tare da gabatar da gamsassun hujjoji kan kowane malami ko ma’aikacin jami’ar ta hanyoyin da jami’ar ta tanada.

Advertisement

Jami’ar ta bayyana cewa wannan mataki na daga cikin manufofinta na ƙarfafa ɗalibai su riƙa bayyana irin waɗannan matsaloli ba tare da tsoro ba, tare da tabbatar da ɗaukar matakan ladabtarwa idan an tabbatar da laifi.

Haka kuma, MAAUN ta musanta rahotannin da ke cewa an jinkirta wa wata ɗaliba karatu na tsawon shekara biyu sakamakon lamarin, ko kuma cewa wata ɗalibar digiri na biyu na cikin waɗanda abin ya shafa, tana mai cewa waɗannan rahotanni ba su da tushe.

Ta buƙaci kafafen yaɗa labarai da jama’a su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafawa ko yaɗawa domin kauce wa yaɗa labaran da za su iya bata sunan mutane ko cibiyoyi ba tare da hujja ba.

Jami’ar na ci gaba da bunƙasa ilimi

Tun bayan kafuwarta ƙarƙashin jagorancin fitaccen ɗan kasuwa kuma mai zuba jari a fannin ilimi, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, MAAUN ta ci gaba da bunƙasa harkokin ilimi tare da jawo ɗalibai daga sassa daban-daban na Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.

Jami’ar ta faɗaɗa shirye-shiryenta na karatu a fannonin likitanci, jinya, injiniya, kimiyyar na’ura mai kwakwalwa, kimiyyar lafiya, kimiyyar zamantakewa da gudanar da kasuwanci, tare da saka hannun jari wajen inganta dakunan gwaje-gwaje, fasahar koyarwa ta zamani da binciken kimiyya.

Advertisement

A cewar jami’ar, tana ci gaba da mayar da hankali wajen samar da ingantaccen ilimi, kare muradun ɗalibai, inganta ɗabi’a da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana a dukkan harkokinta.

A ƙarshe, MAAUN ta sake jaddada cewa alaƙarta da Dr Nasa’i Gwadabe ta ƙare tun watan Mayun 2026, don haka ta bukaci jama’a da kafafen yaɗa labarai su daina bayyana shi a matsayin malamin jami’ar.

 

 

Premium Times 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending