News
Shugaba Tinubu Ya Miƙa Wa Majalisar Dattawa Ƙudirin Gyaran Dokar Ilimin Makarantun Sakandare
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike wa Majalisar Dattawa da ƙudirin dokar gyaran Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Ƙasa (NSSEC) na shekarar 2026, inda ya buƙaci majalisar ta gaggauta amincewa da shi domin inganta yadda ake gudanar da manyan makarantun sakandaren gwamnati a Nijeriya.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar shugaban ƙasar a zaman majalisar da aka gudanar ranar Alhamis.
Kotu ta Aike da Tsohon Shugaban Kotun Da’ar Ma’aikta Gidan Gyaran Hali Na Kuje
A cikin wasiƙar, Tinubu ya bayyana cewa Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ƙudirin a taronta na ranar 30 ga Afrilu, 2026, kafin Ma’aikatar Shari’a ta tantance tare da kammala shirya shi bisa tanadin doka.
Shugaban ƙasar ya ce gyaran dokar wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatinsa na ƙarfafa cibiyoyin ilimi da kuma inganta tsarin tafiyar da manyan makarantun sakandare na gwamnati.
Ya kuma roƙi Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta yi nazari tare da amincewa da ƙudirin cikin gaggawa, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta shugabanci da gudanar da manyan makarantun sakandare a faɗin ƙasar.
Ana sa ran ƙudirin zai taimaka wajen ci gaba da sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya ke aiwatarwa domin inganta tsarin ilimin sakandare a Nijeriya.
-
Uncategorized6 days ago
Samar Da Zaman Lafiya, Ayyukan Ci Gaba Sun Isa Shugaba Tinubu Ya Samu Wa’adi Na Biyu — Kwankwaso
-
News5 days agoAƙalla Mutane 40 Sun Mutu Bayan Kifewar kwale-kwale A Sokoto
-
News1 day ago
Pantami Da Yaransa Sun Fantama Min Ƙarya, Domin Babu Inda Na Ba Shi Haƙuri, Inji Hajiya Naja’atu Muhammad
