Connect with us

News

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Ƙwace Kadarorin Emefiele Masu Darajar Dala Miliyan 2.4

Published

on

Godwin Emefiele 733x400

Kotun Ƙolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin ƙwace kadarori guda bakwai masu daraja tare da kuɗi kusan dala miliyan 2.4 da ake alaƙanta da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.

Hukuncin ya zo ne bayan Kotun Ƙolin ta soke hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Legas ta yanke, wanda ya umarci a sake sauraron shari’ar ƙwace kadarorin.

Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 13 Wani Sabon Harin Da Su Ka Kai A Sokoto

Kwamitin alƙalai biyar na Kotun Ƙolin, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ibrahim Saulawa, sun amince baki ɗaya da ƙarar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar, inda suka jingine hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara tare da mayar da hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Legas.

Kotun ta bayyana cewa EFCC ta gabatar da gamsassun hujjoji da suka nuna cewa kadarorin da kuɗaɗen suna da alaƙa da kuɗaɗen da ake zargin an samo su ta hanyoyin da suka saɓa wa doka, don haka hukuncin ƙwace su ya dace da tanadin doka.

Tun farko dai, Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bayar da umarnin ƙwace kadarorin a ranar 1 ga Nuwamba, 2024. Sai dai Emefiele ya ɗaukaka ƙara, inda Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin tare da umarnin a sake sauraron shari’ar.

Advertisement

Sai dai Kotun Ƙoli ta yi watsi da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara, tare da tabbatar da hukuncin farko na ƙwace kadarorin.

Kadarorin da hukuncin ya shafa sun haɗa da gidaje masu tsada da ke Lekki Phase 1 da Ikoyi a jihar Legas, da kuma kuɗi kusan dala miliyan 2.4 da ake dangantawa da tsohon gwamnan na CBN.

 

 

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending