News
Amincewa Da Naira Biliyan 46 Domin Gyaran Titin Saukar Jiragen Kano Shaida Ce Ta Ƙaunar Shugaba Tinubu Ga Arewa —Kwankwaso
DAGA MUHAMMAD KABIR, KANO
Daraktan Kuɗi na Hukumar Raya Kogin Hadejia-Jama’are (HJRBDA), Dr. Musa Illiyasu Kwankwaso, ya bayyana cewa amincewar da Gwamnatin Tarayya ta yi na ware Naira biliyan 46 domin sake shimfiɗa tare da gyaran titin saukar jiragen sama na biyu a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Mallam Aminu Kano (MAKIA), wata alama ce da ke nuna irin kulawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke bai wa yankin Arewacin Najeriya.
Dr. Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan sanarwar da Ministan Sufurin Jiragen Sama da Bunƙasa Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya yi na amincewa da aikin.
Yadda Ƙudirin Bunƙasa Noma na Magumeri Ke Maido da Fata ga Manoma
Ya ce aikin zai ƙara bunƙasa harkokin sufurin jiragen sama, kasuwanci da tattalin arziki ba a Kano kaɗai ba, har ma da daukacin jihohin Arewa.
A cewarsa, ya kamata al’ummar Arewa su rika yaba wa duk wani aiki na ci gaba da gwamnati ta aiwatar ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba.
“Ina kira ga al’ummarmu, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba, da su gode wa Shugaba Tinubu kan wannan aiki, domin zai amfani yankin Arewa baki ɗaya ta fuskar kasuwanci da bunƙasa tattalin arziki,” in ji shi.»
Ya ƙara da cewa ya kamata al’umma su rungumi al’adar yaba wa ayyukan alheri idan an yi su, maimakon mayar da hankali kan sukar gwamnati kawai.
Tun da farko, Ministan Sufurin Jiragen Sama da Bunƙasa Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ya sanar da amincewar aikin ne yayin ƙaddamar da tashar cikin gida ta Muhammadu Adamu Dankabo da aka sake gyarawa a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano.
A cewar ministan, gwamnatin tarayya ta riga ta saki kusan kashi 60 cikin 100 na kuɗaɗen kwangilar, yayin da kamfanin da aka ba aikin ya fara shirin aiwatar da shi.
Ya bayyana cewa aikin na daga cikin matakan gwamnatin tarayya na inganta Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano tare da ƙarfafa matsayinsa a matsayin babbar cibiyar zirga-zirgar jiragen sama da kasuwanci ga yankin Arewa.
Dr. Kwankwaso ya kuma yabawa Shugaba Tinubu, Shugaban Hukumar Gudanarwar Sufurin Jiragen Sama, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, Ministan Sufurin Jiragen Sama, da Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi, da sauran waɗanda suka bayar da gudunmawa wajen tabbatar da amincewar aikin.
Ya ce idan aka kammala aikin gyaran titin saukar jiragen saman na biyu, Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano zai dawo da matsayinsa a matsayin muhimmiyar ƙofar kasuwanci da tattalin arzikin Arewacin Najeriya.
Sannan ya yi kira ga fitattun ‘yan Arewa, malamai da sarakunan gargajiya da su nuna godiyarsu ga gwamnatin tarayya kan wannan aiki, tare da ƙarfafa al’umma su ci gaba da mara wa duk wani shiri na ci gaba baya.
