News
An Cafke Wani Matashi Bisa Zargin Yunƙurin Satar Adaidaita Sahu A Kano
Jami’an NSCDC sun kama wani matashi mai shekara 27 bisa zargin yunƙurin satar babur Adaidaita Sahu a kan titin IBB da ke cikin birnin Kano.
Mai magana da yawun rundunar ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis cewa wanda ake zargin mai suna Nasiru Sulaiman, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Babura ta Jihar Jigawa.
Kar A Dogara Da Bashi, A Fara Samar da Ayyukan Yi — Okonjo-Iweala Ta Shawarci Shugaba Tinubu
Sanarwar ta ce ana zargin matashin ya yaudari direban Adaidaita Sahun ne ta hanyar aika shi wani saƙo. Bayan direban ya tafi, sai ya cire makullin kunna motar tare da yunƙurin guduwa.
Sai dai wasu jama’a masu sa ido sun lura da abin da ke faruwa, inda suka tare shi kafin ya samu damar tserewa da Adaidaita Sahun.
Daga nan ne aka miƙa wanda ake zargin ga jami’an NSCDC domin ci gaba da bincike.
