News
KANO: Fusatattun Matasa Sun Ƙona Motar Ɗaukar Yashi Bayan Mutuwar Mutane 7 A Rimin Auzinawa
Akalla mutane bakwai ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yankin Rimin Auzinawa, Mangoro Uku, da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.
Wani ganau ya shaida wa Arewa Radio 93.1 cewa hatsarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Laraba.
Jihar Kano Ta Samu Tikitin Buga Gasar Wasanni Ta National Sports Festival 2026
Majiyar ta ce wasu daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu ƙananan yara ’yan makaranta ne, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin alhini da jimami.
Rahoton ya ce bayan faruwar hatsarin, wasu fusatattun matasa sun banka wa motar ɗaukar yashi da ake zargin tana da hannu wajen haddasa hatsarin wuta.
Lamarin ya haifar da tashin hankali a yankin, yayin da ake jiran jami’an tsaro su isa wurin domin shawo kan lamarin da kuma gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin.
Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani daga hukumomin tsaro kan matakin da aka ɗauka ko kuma cikakken bayani game da hatsarin ba.
