Connect with us

News

Majalisar Tarayya Ta Miƙa Ƙudirin ’Yan Sandan Jihohi Ga Majalisun Jihohi 36

Published

on

Untitled design 2025 10 19T120638.147

Majalisar Dokokin Tarayya ta miƙa ƙudirin sauya Kundin Tsarin Mulkin Najeriya da ya shafi kafa rundunar ’yan sandan jihohi ga majalisun dokokin jihohi 36 domin nazari da amincewa.

Magatakardar Majalisar Dokokin Tarayya, Kamoru Ogunlana, ya ce an miƙa ƙudirin ga majalisun jihohin ne a ranar Laraba, 16 ga Satumba, 2026, bisa umarnin shugabannin majalisar.

Dakarun Soji Sun Kubutar Da Mutane 31 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Jihohin Katsina Da Kebbi

Ya ce ana sa ran majalisun dokokin jihohin za su nazarci ƙudirin tare da bayyana matsayinsu cikin kwanaki 30, ko da yake Kundin Tsarin Mulkin Najeriya bai kayyade wa’adin da majalisun jihohi za su kada da ƙuri’arsu ba.

A cewar tanadin Sashe na 9 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, sauya kundin tsarin mulki na bukatar amincewar aƙalla kashi biyu bisa uku na majalisun dokokin jihohi, wato majalisu 24 daga cikin 36, kafin a kai matakin na gaba.

Ƙudirin kafa ’yan sandan jihohi na daga cikin muhimman sauye-sauyen da ake son yi a tsarin mulkin ƙasar. Manufarsa ita ce samar da tsarin tsaro da zai kusantar da aikin ’yan sanda ga al’umma da kuma bai wa jihohi ƙarin rawa wajen kula da tsaron jama’a.

Advertisement

 

 

CHANNELSTV 

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending