Connect with us

News

Jami’an Ƴansanda 98 Ne Suka Mutu A cikin Watanni 10 A Sassan Najeriya — Rahoto 

Published

on

Police burial 768x462
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya gano cewa jami’an rundunar ’yan sandan Najeriya 98 ne suka rasa rayukansu a jihohi 21 na ƙasar tsakanin watan Janairu zuwa Oktoban 2026.

Jaridar ta ce ta tattara bayanan ne daga rahotanni daban-daban da hukumomin tsaro suka tabbatar, inda binciken ya nuna cewa jami’an sun mutu sakamakon hare-haren ’yan bindiga da ’yan ta’adda, haɗurran mota da kuma harbin kuskure daga takwarorinsu.

Jami’an Ƴansanda Sun Bankado Wurin Buga Jabun Kudi Na Dalar Amurka A Ondo

Binciken ya nuna cewa Jihar Yobe ce ta fi yawan asarar jami’an ’yan sanda, inda aka samu mutuwar jami’ai 17, sai jihohin Zamfara da Kebbi da suka rasa jami’ai 14 kowannensu.

Haka kuma, jami’ai biyar ne suka mutu a Jihar Katsina, yayin da Taraba da Borno suka rasa jami’ai huɗu-huɗu.

Sauran jihohin da aka samu mutuwar jami’ai uku-uku sun haɗa da Rivers, Sokoto, Filato, Enugu, Legas da Imo.

Advertisement

Dangane da waɗanda suka haddasa mutuwar jami’an, binciken ya ce ’yan ta’adda ne suka kashe jami’ai 35, yayin da ’yan bindiga suka hallaka 29.

Haka kuma, mayaƙan Boko Haram sun kashe jami’an ’yan sanda 22 a cikin wa’adin da binciken ya ƙunsa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro da barazanar hare-hare a sassa daban-daban na Najeriya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending