Connect with us

News

Najeriya na fuskantar barazanar da za ta iya rusa ta – Babban Bankin Duniya

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Babban Bankin Duniya World Bank, a jiya Laraba ya yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar barazanar da za ta iya rusa ta.

Advertisement

World Bank ya yi gargadin cewa idan Najeriyar ta gagara gyara tsarin tara harajinta da kuma mayar da hankali akan wasu bangarorin domin bunƙasa kuɗaɗen shigarta, to ƙuɗaɗen shigarta za su ci gaba da raguwa.

Jaridar Punch ta ce wani babban jami’i a Babban Bankin Duniyar, Mr Rajul Awasthi ne ya bayyana haka a wani taro akan muhimmanci yi wa tsarin haraji kwaskwarima domin cigaban kasa, wacce wata kungiyar sa ido kan tattalin arzikin Najeriya ta shirya.

Advertisement

Sannan jami’in ya haƙiƙance cewa dole Najeriya ta cire tallafin man fetur baki daya nan gaba.

World Bank ya bayyana cewa duk da cewa farashin man fetur na ƙaruwa a kasuwannin duniya, Najeriya ba ta samu cin gajiyar wannan dama ba saboda maƙudan kudaden da take kashewa akan rarar man fetur.

Advertisement

Wannan gargadi yana zuwa ne a lokacin da ƙudaden shigar Najeriya ke raguwa kuma tana cigaba da biyan tiriliyoyin nera akan tallafi man fetur da matsalolin tattalin arziki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending