News
Jihar Jigawa ta cika shekaru 31 da kafuwa a matsayin jiha
DAGA KHADIJA ABDULLAH MUHMD
Jigawa jiha ce cikin jihohi 36 dake Nigeria, tana cikin yankin Arewaci, wacce aka cire ta daga tsohuwar jihar Kano a shekarar 1991, kuma tayi iyaka da wani yanki na ƙasar Niger. Dutse ne babban birnin jihar ta Jigawa.
Ƴan Bindiga Sun Datse wa Manomi Hannayensa a Zamfara
Jihar Jigawa nada Ƙananan hukumomi guda ashirin da bakwai (27) da suka hada da:
– Auyo
– Babura
– Biriniwa
– Birnin Kudu
– Buji
– Dutse
– Gagarawa
– Garki
– Gumel
– Guri
– Gwaram
– Gwiwa
– Hadejia
– Jahun
– Kafin Hausa
– Kaugama
– Kazaure
– Kiri Kasama
– Kiyawa
– Maigatari
– Malam Madori
– Miga
– Ringim
– Roni
– Sule Tankarkar
– Taura
– Yankwashi
Akwai masarautun gargajiya guda biyar a wannan jiha ta Jigawa da suka hada da:
– Masarautar Dutse
– Masarautar Kazaure
– Masarautar Hadejia
– Masarautar Ringim
– Masarautar Gumel
Daga lokacin da aka ƙirƙir wannan jiha ta Jigawa zuwa yau (2022), ta yi gwamnoni guda takwas, ga Sunayensu kamar haka:
– Manjo Janar Olayinka Sule
– Barr. Ali Sa’adu
– Brigadier General Ibrahim Aliyu
– Colonel Rasheed Alade Shekoni
– Colonel Abubakar Zakariyya Maimalari
– Alhaji Ibrahim Saminu Turaki
– Alhaji Sule Lamiɗo
– Alhaji Mohammad Badaru Abubakar, mon, mni
Ko wanene sabon gwamnan Jigawa a shekarar 2023? Allah masani !!
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
