News
Yan sanda sun kama ‘sojan boge’ da zargin yi wa mata fashi a Jihar Legas
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dakarun bincike na rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Legas sun kama wani mutum da zargin bayyana kan sa a matsayin soja don aikata fashi da damfarar ‘yan mata.
Sojan bogen mai shekara 39 kan bayyana kan sa a matsayin dillalin tallata kayayyaki sannan ya gayyaci mata don gwada basirarsu, amma daga ƙarshe sai ya ƙwace musu kayayyaki ta hanyar ritsa su da bindiga, a cewar sanarwar da rundunar ta fitar ranar Lahadi.
YANZU-YANZU: Atiku ya sauka a Kano domin karɓar Shekarau zuwa PDP
Sanarwar ta ce an kama mutumin bayan ɗaya daga cikin waɗanda ya yi wa fashin ta kai rahoton ƙwace mata mota ƙirar Lexus RX330.
Binciken da rundunar ta gudanar ya gano ƙarin motar alfarma da keken ɗinki da na’urar cire kuɗi ta POS a wajensa.
Ta nemi masu waɗannan kayayyaki da su gabatar da kansu gare ta don karɓar kayayyakinsu, inda ta ce za ta gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike a kansa.
