Connect with us

News

Majalisar Dattawa Ta Tona Wadan da Suka fi ‘Yan Siyasa Sata da Rashin Gaskiya

Published

on

Majalisa

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

 

 

 

Advertisement

 

 

 

 

Kwamitin sauraron korafi na majalisar dattawa yace ya gano cewa ma’aikatan gwamnati sun fi kowa tafka rashin gaskiya a duk Najeriya.

An ruwaito shugaban kwamitin, Sanata Ayo Akinyelure yana cewa bincikensu ya nuna masu ma’aikatan gwamnatin sun fi ‘yan siyasa barna a kasar nan.

Advertisement

Ayo Akinyelure mai wakiltar yankin jihar Ondo a karkashin jam’iyyar PDP, yayi wannan bayani ne a wajen wani taron karawa juna sani da aka shirya.

An yi wannan taro na kwana biyu ne a garin Abuja domin fadakar da ma’aikatan gwamnati da na kamfanonin ‘yan kasuwa a kan aikin ofis.

Sanatan ya ce kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya iya nasara wajen yaki da rashin gaskiya, dole ya kawo karshen barnar da ma’aikatan gwamnati suke yi.

An ruwaito Ayo Akinyelure yana cewa abin da ya sa ma’aikatan gwamnati suke aikata ba daidai ba shi ne saboda sun fi ‘yan siyasa dadewa a bakin aikinsu.

A dalilin shekarun da ma’aikata suke dauka a ofis, shiyasa ake fama da sata da rashin gaskiya.

‘Dan siyasar yake cewa ma’aikatan gwamnati sun kware a aikinsu domin sun yi shekaru 35, alhali ‘yan siyasa sai sun nemi tazarce bayan shekaru hudu.

Advertisement

A cewarsa, kafin a iya samun shugabanci nagari da gaskiya a wajen aiki, ya zama dole a rika bin doka a kamfanonin ‘yan kasuwa da ma’aikatun gwamnati.

A cikin matsalolin da al’umma ke fama da su yau, Akinyelure yace akwai rashin gaskiya, cin hanci, rashawa, sata, badakalar kwangiloli da raunin bankuna.

Baya ga wadannan matsaloli da suka shafi tattalin arziki, ‘dan majalisar yace Najeriya na yaki da rashin tsaro, wanda ya jawo ake rasa rayuka da dukiyoyi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending