News
Kotu Ta Daure Wani Mutum Da Damfarar Naira Miliyan 1.7 A Maiduguri
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Mai shari’a Umaru Fadawu na babbar kotun jihar Borno dake Maiduguri, ya yankewa Alkali Bukar Mohammed hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari bisa samunsa da laifin karkatar da dukiyar jama’a har naira miliyan 1,700,000 (Miliyan daya, Naira dubu dari bakwai).
Yan sandan Kano sun kama mutane 331 a cikin wata guda
An yanke masa hukunci ne a ranar Juma’a, 9 ga watan Satumba, 2022 bayan ya amsa laifuka guda daya, wanda ke da alaka da karkatar da dukiyar jama’a, bayan da hukumar EFCC shiyyar Maiduguri ta gurfanar da shi a gaban kuliya.
Advertisements
