Connect with us

News

Mutum 19 sun mutu a hadarin mota a Abuja

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

An tabbatar da mutuwar mutum 19 a wani mummunan hadarin mota a da ya auku a kan hanyar Yangoji zuwa wagwalada a Abuja babban birnin Najeriya.

Da yake tabbatar wa da kamfanin dillacin labaran kasar NAN adadin wadanda suka mutun, mai rikon kwaryar babban kwamandan hukumar Mr kiyaye hadura ta kasa Mista Dauda Biu, ya ce hatsarin ya rutsa ne da motoci uku.

Zaben 2023: Kungiyar NUJ Ta Gargadi Membobi Akan Hada Kai Da Yan Siyasa

Advertisement

Ya kara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum 31, inda mutum takwas suka samu munanan raunuka, yayin da kuma 19 suka mutu.

Ya ce bincike ya nuna cewa gudun wuce-kima tare da neman wuce juna ne ya haddasa aukuwar hatsarin.

Ana dai yawan fuskantar hadaran mota a manyan titunan Najeriya, wanda ake dora alhakin hakan kan rashin kyawun tituna, da tukin ganganci da uwa uba gudun da ya wuce kima da masu ababen hawa ke yi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending