News
Gwamnatin Najeriya ta ba da Hutun Mauludi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Gwamnatin Najeriya ta ayyana Litinin 10 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu don murnar bikin Mauludin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu (Tsira da Amincin Allah su Tabbata Gare shi).
Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, wanda ya sanar da haka a madadin gwamnatin tarayyar Najeriya ya taya al’ummar Musulmi a gida da ƙetare murnar sake ganin wannan biki na bana.
Ƙungiyoyin fansho da na ƙwadago sun yi zanga-zanga a Kano
Ya gargaɗi duk ‘yan Najeriya su rungumi son juna da haƙuri da jure zama da juna da jimiri waɗanda halaye ne da Annabi Muhammadu ya koyar, inda ya ƙara da cewa yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya da tsaro da zaman tare a Najeriya.
Sanarwar da Babban Sakataren ma’aikatar Dr. Shuaib Belgore ya fitar ta ambato Minista Aregbesola na yin kira ga ‘yan Najeriya musamman al’ummar Musulmi su guji ayyukan tarzoma da rashin bin doka da sauran ayyukan laifi.
Da yake kira a dakatar da duk wasu halaye da za su kawo rarrabuwar kai a faɗin ƙasar, ministan ya kuma buƙaci duk ‘yan Najeriya da kuma musamman matasa su rungumi ɗabi’un aiki tuƙuru da halayyar zaman ga ‘yan’uwansu bil’adama ba tare da la’akari da bambancin addini ko aƙida ko rukunin jama’a da ƙabila ba.
Aregbesola ya kuma buƙaci ‘yan Najeriya su kasance masu tunanin yanayin tsaro, kuma su kai rahoton duk wani mutum ko aikace-aikacen da ba su amince da take-takensu ga hukumomin tsaro mafi kusa.
BBC
