News
An gudanar da taron waɗanda suka shahara a shafukan sada zumunta a Kano
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An gudanar da taron waɗanda suka shahara a shafukan sada zumunta a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, inda aka tattauna yadda za a shawo kan matsalar yaɗa kalaman ƙiyayya da yaɗa labaran ƙarya a intanet yayin da ake tunkarar zaben 2023.
Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa CITAD ce ta shirya taron inda ta gayyaci ƙwararru da masu ruwa da tsaki a fannin fasahar sadarwa inda aka gabatar da lakcoci a fannoni daban-daban.
EFCC ta sake gurfanar da tsohon akanta janar Ahmad Idris
Mutanen da suka yi fice a dandalin sada zumunta da saraun masu ruwa da tsaki a wannan fanni ne aka gayyata wannan taro inda aka gabatar da jawabai iri daban-daban kan yadda za a magance matsalar kalaman ƙiyayya da kuma labaran jabu dangane da zabuka a Najeriya.
Shugaban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Kashere jihar Gombe Farfesa Umar Pate na daga cikin wadanda suka gabatar da maƙala.
Dr Kole Shatimma shugaban gidauniyar MacArthur a Najeriya ya ce shafukan sada zumunta suna da muhimmanci ga zaben ƙasar don haka yana da kyau a fahimta da masu ta’ammali da su.
Ko me mahalarta wannan taro suka fahimta daga irin jawaban da aka gabatar.
Bayanai na cewa labaran ƙarya da wasu ke yaɗawa a shafukan sada zumunta na ci wa hukumar zabe mai zaman kanta INEC tuwo a ƙwarya, inda rahotanni suka ambato shugaban hukuma na cewa sun tashi haiƙan don yaƙar wannan matsala tun kafin ta haifar musu da cikas.
Shafukan sada zumunta dai, akwai wasu da ake kira sojojin-baka ko kuma ƴan soshiyal midiya wadanda ba su da aiki sai koda dan siyasa da faɗin alherinsa, al’amarin da yake jawo ce-ce-ku-cen da ake ganin ya kamata a rika yin taka tsan-tsan don kada ya haifar da fitina.
