Connect with us

News

Buhari zai tafi London domin a duba lafiyarsa

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

Advertisement

 

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai kama hanyarsa zuwa London a yau dinnan domin a duba lafiyarsa.

Advertisement

Kakakin shugaban, Femi Adesina a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya ce ana saran Buhari zai koma gida a cikin mako na biyu na watan Nuwamba.

Shugaban Najeriyan ya sha tafiya Landan domin duba lafiyarsa tun lokacin da ya fara jagorantar kasar.

Advertisement

A 2017, Shugaban ya kwashe kwanaki 150 a Burtaniya a wata tafiyar duba lafiyar da ba a bayyana abin da ke damun shi ba.

Buhari ya kara komawa Burtaniya a watan Mayun 2018 domin ganin liktansa, inda ya yi kwana hudu kacal a kasar.

Advertisement

A watan Nuwambar 2020 ne, mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari, ta ce akwai bukatar inganta bangaren lafiya a Najeriya domin a rage tafiye-tafiyen neman magani kasashen waje

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending