News
Maki 150 mafi ƙaranci FUD ke buƙata a shekarar karatu ta 2022/2023
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Jami’ar tarayya ta Dutse, ta sanar da maki 150 a matsayin mafi ƙaranci na samun gurbin karatu na shekarar karatu ta 2022/2023 ga ɗaliban da su ka sanya jami’ar a zaɓin farko.
Jami’ar ta kuma sanar da cewa a yau Litinin, 31 ga Oktoba zuwa 4 ga Nuwamba za ta yi aikin tantance waɗanda ke neman gurbin karatu a jami’ar ta hanyar JAMB, DE da kuma IJMB.
Buhari zai tafi London domin a duba lafiyarsa
A sanarwar da Kakakin jami’ar, Abdullahi Bello ya fitar, ya ce jami’ar na shawartar ɗaliban da ke naman gurbin karatu a jami’ar na 2021 da su yi maza su kammala tantance wa kafin a tafi yajin aiki da su yi maza su yi kafin 4 ga watan Nuwamba.
Ya ce a na shawartar masu neman guraben karatu da su shiga shafin yanar gizo na visit putme@fud.edu.ng domin ƙarin bayani.
