Hukumar da ke yaki da masu ta’ammali da miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce ta kama mutum 130 dauke da miyagun kwayoyi a jihar Kaduna a watan Oktoba.
Hukumar wadda ta ce bakwai daga cikin mutanen mata ne, kwayoyin sun kai nauyin kilogram 1,728.536.
Shugaban PDP Na Zamfara, Sani Ahmad, Ya Rasu
Kwamandan hukumar a jihar ta Kaduna, Mr Umar Adoro, ya gaya wa kamfanin dillancin labarai News Agency of Nigeria yau Laraba cewa, hukumar tasa ta kuma rushe wurare 20 da suka yi kaurin suna wajen hada-hadar miyagun kwayoyi.
Haka kuma shugaban ya kara da cewa sun yi nasarar rufe gidaje bakwai da ke da alaka da miyagun kwayoyi.
Adoro ya ce hukumar ta kuma gano naira dubu N300 ta takardar naira N1,000 daga wadanda aka kama masu safarar miyagun kwayoyi.
Kwamandan ya ce miyagun kwayoyin da aka kwace sun kunshi ganyen wiwi kilogram 1,388.811 sai hodar Iblis ta koken kilogram 0.019 da hodar Iblis ta heron kilogram 0.001 da Tramadol mai nauyin kilogram 7.666 sai wasu nau’in kwayoyin da nauyinsu ya kai kilogram 331.786 da kuma miyagun magungunan maye da ake harhadawa da nauyinsu ya kai kilogram 0.253.
Hukumar ta NDLEA ta kuma ce ta gudanar da tarukan wayar da kan jama’a a makarantun sakandire a
Kafanchan da Kaduna da Zaria bayan wasu biranen da garuruwa domin fadakar da jama’a kan ilolon miyagun kwayoyi.
