News
Masu ruwa da tsakin APC na karamar hukumar Doguwa sun ziyarci Sulen Garo
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugabannin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC na karamar hukumar Doguwa a jihar Kano, sun ziyarci dan takarar mataimakin gwamnan Kano na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023 mai zuwa, Murtala Sule Garo, bayan rikicin da ya faru tsakanins da dan majalisar tarayya na Doguwa da Tudun Wada, Alasan Ado Doguwa.
Sanata Ms’ud El-Jibril Doguwa shi ne ya jagoranci tawagar tare da dan majalisar jiha mai wakiltar Doguwa, Hon. Salisu Mohammed da tsohon kwamnina Hon. Usman Sule Riruwai da mataimakin shugaban Jam’iyya Alh. Shehu Maigari, da shugaban karamar hukumar Doguwa, Alh. Mahmuda Hudu da Shugaban Jam’iyyar APC na Doguwa da sauran Jagororin Jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa, shugabbannin sunyi bayani na nuna rashin jin dadin su da kuma rokon Murtala Sule Garo yayi hakuri, sannan sun tabbatar da zasu dauki matakin daya dace tun daga tushe.
