Connect with us

News

Ganduje ba ya cikin gwamnonin da za su biya ma’aikata kuɗi hannu da dukiyar sata’

Published

on

Ganduje

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Gwamnatin Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta musanta rahoton da ke cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na cikin gwamnonin da ke ƙoƙarin halsta kuɗin haram ta hanyar biyan ma’aikata albashi a hannu maimakon ta banki.

Advertisement

Kwankwaso Ya Shirya Karbar Alhassan Doguwa, Inji Rurum

Martanin na zuwa ne bayan wata kafar yaɗa labarai ta intanet ta yi iƙirarin cewa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta saka wa Ganduje ido tare da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle da Gwamnan Ribas Nyesom Wike saboda sun ɓoye garin biliyoyin kuɗi a wasu wurare.

Advertisement

Kafin haka, Shugaban EFCC Abdulrasheed Bawa ya faɗa wa Daily Trust cewa biyu daga cikin gwamnonin sun fito daga arewacin ƙasar, yayin da ɗaya ya fito daga kudanci – amma bai faɗi sunayensu ba.

“Duk da cewa EFCC ba ta faɗi sunan gwamnonin ba amma Sahara Reporters ta yi gaban kanta wajen yin iƙirari maras tushe,” a cewar sanarwar da Kwamashinan Yaɗa Labarai na Kano Muhammad Garba ya fitar.

Advertisement

“Saboda haka ne ya nemi ta janye labarin tare da neman afuwa, wanda idan ba ta yi haka ba gwamnatin za ta kai ƙara kotu.”

BBC HAUSA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending