Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya ta gabatar da sabbin tuhume-tuhume kan Nnamdi Kanu

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sake gabatar da tuhumar ta’addanaci mai laifuka bakwai kan jagoran ‘yan awaren Biafra, Nnamdi Kanu, a gaban Babbar Kotun Tarayya.

 

Advertisement

A ranar 13 ga watan Oktoba ne Kotun Ɗaukaka Ƙara ta umarci a saki Kanu shugaban ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) daga gidan yari sakamakon abin da ta ce an gurfanar da shi ba bisa ƙa’ida ba.

Ɗalibin BUK ya zama shugaban ƙungiyar LAWSAN ta Najeriya

Amma gwamnati ta ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli kan hukuncin na Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Advertisement

 

Tun a watan Afrilun 2022 ne kotun ta yi watsi da tuhuma takwas cikin 15 da gwamnatin ke yi wa Kanu da suka haɗa da tayar da hankali da tsokanar Shugaba Muhammadu Buhari da cin amanar ƙasa.

Advertisement

 

Sai dai har yanzu ba a saki jagoran ba, inda yake ci gaba da zama a gidan yari a Abuja, babban birnin ƙasar.

Advertisement

 

Gwamnatin ta shigar da sabbin tuhumar ne yayin da ake jiran Kotun Ƙoli ta fara sauraron ƙarar da ta ɗaukaka kan hukuncin da ya ce a saki Kanu.

Advertisement

 

A watan Yunin 2021 ne gwamnati ta kama tare da sake gurfanar da Nnamdi Kanu a gaban kotu bayan ya gudu daga ƙasar ta hanyar karya dokokin belin da kotu ta bashi a gurfanarwar farko da aka yi masa.

Advertisement

 

Jami’an tsaro a Najeriya sun sha zargin ƙungiyar IPOB da kashe jami’ansu da kuma kai hare-hare kan mazauna yankin kudu maso gabashin ƙasar, inda ƙabilar Igbo suka fi rinjaye, yankin da take so ta kafa ƙasar Biafra idan ta ɓalle daga Najeriya.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending