Connect with us

News

Ba Ni Da Asusun Banki A Ko’ina Idan Ba A Najeriya Ba— Kwankwaso

Published

on

Kwankwaso

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba shi da wani asusun banki a wata ƙasa a faɗin duniya idan ba Najeriya ba.

EFCC na neman A.A Zaura ruwa-a-jallo

Kwankwaso ya bayyana haka ne ranar Lahadi a yayin wata hira da ‘yan takarar shugaban ƙasa da Arise TV ta shirya.

Advertisement

“Ba ni da asusun banki a ko’ina a faɗin duniya idan ba a Najeriya ba. Ba ni da kasuwanci a wata ƙasa saboda ina so in gina ƙwarin guiwa ga mutanen da suka yadda da mu”, in ji Kwankwaso.

Da yake amsa tambaya game da yadda zai inganta ilimi idan ya ci zaɓe, Kwankwaso ya ce: “Gwamnatinmu ta yi imani cewa hanyar da ta fi kyan bi ita ce a zuba jari a ilimi. Dole a yaƙi cin hanci, saboda shi ne babbar matsalarmu. Yaƙi da cin hanci a ɓangaren ilimi zai tabbatar da tafiyar komai daidai.

Advertisement

“Za mu yi dukkan abin da ya kamata don samar da ilimi mai inganci. Za mu shigo da wasu manufofi da za su inganta lafiya ta hanyar NHIS. Za mu tabbatar kowane ɗan Najeriya yana iya zuwa asibiti.

“Manufarmu za ta kasance mu horar da ‘yan Najeriya da yawa. Za mu ƙarfaga gwiwar ‘yan Najeriya don su kammala karatu su yi

Advertisement

aiki a kasuwar Najeriya”, ya ƙara da haka.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

LABARAI 24

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending