Shugaban China Xi Jinping ya isa Saudiyya a ziyara irin ta ta farko da ya taɓa kai wa masarautar cikin shekaru shida.
Ana sa ran shugaba Xi zai gana da Sarki Salman bin Abdul’Aziz al-Sa’ud, da kuma Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman, za kuma su halarci taron koli na yankin gulf.
China babbar aminiya ce ga Saudiyya ta fuskar kasuwanci, tana kuma neman ƙara faɗaɗa hakan a ƙasar.
Ziyarar na zuwa ne, daidai lokacin da a hukumance dangantaka tsakanin Saudiyya da Amurka ta yi tsami, yayin da ita ma China da Amurkar alakar ta ƙara dagulewa fiye da shekarun baya.
